fbpx
Friday, April 23
Shadow

An kama wani mutum da kawunan mutum biyu a Jihar Ondo

An kama wani mutum mai matsakaicin shekaru, Hassan Saka a jihar Ondo da kawunan mutum biyu a ranar Litinin, 1 ga Maris.

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ne suka yi nasarar kamun a jihar.

An gano abubuwan ne a cikin wata mota akan hanyar Owo / Akure, wadanda aka boye a cikin kwali mai kalar ruwan kasa.

Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro, ya ce jami’an NSCDC sun mika Saka ga‘ yan sanda.

Ya kara da cewa a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *