fbpx
Friday, May 14
Shadow

An kama wani mutum mai shekaru 42 da ake zargi da lalata diyarsa mai shekaru 9

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 42, Segun Olusoji, bisa zargin lalata da‘ yar sa mai shekaru tara a yankin Ilasamaja da ke jihar.

Da yake gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu, Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu, ya ce wanda ake zargin yakan tayar da’ yarsa daga bacci don yayi lalata da ita.

Wani Oluwafunmibi Ojewale ne ya gabatar da karar a kan wani Segun Olusoji, mai shekaru 42, a hedikwatar rundunar‘ yan sanda da ke Itire kuma daga baya aka tura shi zuwa ga SCIID, Yaba, domin gudanar da bincike cikin tsanaki.

Lokacin da aka yi masa tambayoyi, wanda ya shigar da karar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin yana yin lalata da diyarsa ‘yar shekara tara.

Haka kuma yarinyar tabbatar da cewa mahaifin yakan tashe ta da daddare don yayi lalata da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *