fbpx
Saturday, April 17
Shadow

An kama wani mutum mai shekaru 65 da laifin lalata yarinya ‘yar shekara 10 a Jihar Kwara

Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Kwara, ta cafke wani tsoho dan shekaru 65, mai suna Samuel Darisa, bisa zargin lalata da yarinya ‘yar shekara 10.

Kakakin rundunar, Babawale Afolabi, wanda ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar NSCDC da ke Ilorin a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris, ya ce wanda ake zargin ya aikata hakan ne a yankin dam din Agba, GRA, na babban birnin kasar inda yake aiki a matsayin mai gadi.

Babawale ya ce, an cafke wanda ake zargin ne bayan wani makwabcinsa wanda ya kama su a yayin da suke aikata laifin, ya ba su rahotannin sirri.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, yana mai cewa karamar yarinyar ta amince da aikata hakan.

Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin bayan an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *