fbpx
Thursday, May 6
Shadow

An kama wani mutum mai shekaru 68 da ake zargi da yi wa yarinya ’yar shekara 7 fyade a Jihar Anambra

Yan sanda reshen Jihar Anambra sun kama wani tsohon dan shekaru 68, mai suna Linus Onuzulike bisa zargin yiwa wata yarinya yar 7 fyade a garin Abagana da ke cikin karamar hukumar Njikoka.

An gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutum goma sha biyar kan laifuka daban-daban a shalkwatar rundunar ’yan sandan.

Kakakin ‘yan sanda, Haruna Mohammed, ya kuma tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 24 a kan fyade da aka yi wa yarinya‘ yar shekara 16.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa bisa radin kansa, ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan bincike.

Da yake magana da manema labarai, Mista Onuzulike, ya musanta zargin fyade, yana mai cewa mahaifiyar wanda aka yi wa fyaden ce ke zargin sa bayan sun samu rashin fahimta.

Ya kara da cewa bayyan Benedict ta zarge shi, ya gayamata suje ofishin yan sanda domin a gudanar da bincike da kuma gwajin asibiti domin a tabbatar idan shi ya aikata ko sabbanin haka.

Amma sai taki kuma ta gudu da yar ta, bayan wasu kwanaki sai kwatsam naga tazo da yan sanda a gidana tana ikirarin cewa ni nayi wa yar ta fyade, daga nan ne jami’an suka damke ni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *