fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An kama wani shahararren barawo da laifin satar motar gwamnatin jihar Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun cafke wani sanannen barawon mota da ake zargi da sace wata mota kirar Hilux mallakar gwamnatin jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, ya ce wanda ake zargin, Hayatu Bashir ya sace motar Inda aka ajiye ta, cikin masallaci da ke GRA a lokacin sallar Juma’ar da ta gabata.

PPRO ya bayyana cewa motar mallakar kwamatin dindindin ne na jihar Katsina kan inganta dangantakar manoma da makiyaya a jihar Katsina.

An tattaro cewa bayan ya sace motar a GRA a babban birnin jihar, ya tuka ta zuwa garin Malumfashi a karamar hukumar Malumfashi na jihar.

An yi zargin yana shirin yiwa motar gunduwa-gunduwa domin sayar da ita ga yan gwangwani yayin da tawagar ‘yan sanda suka zo kan shi suka cafke shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *