fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

An kama wasu jami’an EFCC na bogi a Legas

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, ta cafke wasu mutane uku dake dake shiga cewa su jami’anta ne.

Wadanda ake zargin sun shiga wani aiki ba bisa ka’ida ba wanda ake zargin sun aiwatar da umarnin Kotu na karya a New Horizon Estate, Lekki.
Shugaban Ofishin shiyya na EFCC, Ghali Ahmed, wanda ya tabbatar da kamun nasu, ya ce an kama su ne a yayin da suke ba da aiwatar da umarnin Kotu wanda ake zargin sun fito ne daga Kotun Majistare ta Mushin a kan wane mutum.
Wadanda ake zargin sun hada da Pascal Ugwu Chijoke, Sodiq Ibrahim Adekunle da Edwin Bassey, wani Sufeton ‘yan sanda, da ke nuna kansu a matsayin jami’an EFCC, ana zargin sun kutsa kai cikin gidan da suke niyyar da dukkan kayan aikin irin wanda EFCC ta saba kai wa, suna sanye da jaket din EFCC da jabun takardu.
Ahmed ya kara gargadin ‘yan Najeriya da su yi hattara da masu yaudara da ke amfani da sunan hukumar da kyau don yaudarar wadanda ba su sani ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *