fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An kama wasu maza biyu da ake zargi da yiwa yar makwabcinsu mai shekaru 16 fyade 

Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun sun cafke wasu maza biyu da ake zargin yiwa yar makwabcinsu mai shekaru 16 fyade.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya fitar, an kama wadanda ake zargin Anthony John 35yrs da Jimoh Idowu 21 ne bayan wani korafi da yarinya ta shigar a hedkwatar reshen owode-Egba, wacce ta bayar da rahoton cewa tana gida tare da kannenta a kauyen Efunye ta hanyar Owode-Egba, lokacin da wadanda ake zargin su biyu, suna zaune a gida daya tare da su suka kutsa kai cikin gidan nasu da misalin karfe 2:00 na dare suka yi awon gaba da ita zuwa dakin Anthony, Inda nan ne suka kyata mata haddi.

Bayan rahoton, DPO na Owode-egba, Csp Ediae Mathew ba tare da bata lokaci ba ya aika da jami’an bincikensa zuwa inda aka cafke wadanda ake zargin nan take.

A yayin bincike, mutanen biyu da ake zargin sun amsa laifinsu ba tare da wata gardama ba.

An kai wanda aka yi fyaden zuwa babban asibitin Owode-egba don kula da lafiyar ta.

Oyeyemi ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Cp Edward Ajogun ya ba da umarnin a mika wadanda ake zargin zuwa sashin yaki da fataucin mutane da kuma bautar da yara don ci gaba da bincike da kuma himma wajen hukunta su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *