fbpx
Saturday, April 17
Shadow

An kama wasu mutane 4 kan zargin yiwa wata mata fyade da kuma kashe ta a Jihar Kwara

Hukumar tsaro dake baiwa farar hula kariya (NSCDC) reshen jihar Kwara, ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi a garin Esie da Ijan, karamar hukumar Irepodun da ke jihar kan zargin yiwa wata mata fyade da kuma kashe ta.

Kakakin NSCDC a jihar, Babawale Zaid Afolabi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 5 ga Afrilu, ya ba da sunan wadanda ake zargin kamar haka; Adams Sodiq mai shekaru 19, Rasaq Rasheed, 16, Lukman Quadri, 15, da Billiaminu Qayum, 16.

A cewar kakakin, wani jami’i mai suna, Babatunde Azeez, a ranar 2 ga Afrilu, 2021, da misalin karfe 5:00 na safe ya samu korafi daga Sakataren, Fulani / Bororo a yankin Esie da Ijan, Alhaji Musa Waziri, game da wata mata da ta bata mai suna Aishat Sanni.

Daga baya an gano gawar matar da ta ɓace a cikin daji kuma an kama mutane huɗun da ake zargi bayan bincike na gaskiya, ya alakanta su da kisan.

Mai magana da yawun NSCDC din ya ce an mika lamarin ga ‘yan sanda, wadanda ke kula da shari’ar kisan kai domin cigaba da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *