fbpx
Monday, May 10
Shadow

An kama wasu ‘yan sanda uku da laifin karbar N153,000 daga wani dalibin Jami’ar LASU dake Jihar Legas

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke wasu jami’anta guda 3 wadanda suka karbi kudi N153,000 daga wani dalibin jami’ar jihar Legas (LASU) mai suna Hezekiah Oluwaponmile.

Yan sandan, wadanda ke hade da PMF16, an bayyana sunayen su kamar haka; Sufeto Sunday John mai lamba AP / NO. 310332, Sajan Jimoh Asimiya mai lamba F / NO. 447461 da kuma Sajan Solomon Adedapo mai lamba F / NO. 498346 SGT.

Oluwaponmile ya je shafukan sada zumunta ne a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, don ba da rahoton yadda jami’an suka tilasta shi “da bindiga” ya tura masu N153,000 ta hanyar wakilin POS.

Da yake bada labari (wanda abun ya shafa), yace a lokacin da suka tare su, ya gaya masu cewa shi dalilin LASU ne amma duk da haka suka ce ya bude wayarsa.

Bayan ya bude wayarsa sai suka ce ya basu N1m, sai yace masu bai kudi, suka tilasta masa bude manhajar bankinsa, inda suka ga yana da N288,000 kuma suka ce masa ya tura masu N250,000 duk da cewa bai san laifin da ya aikata ba.

Bayan tattaunawa da roko, dalibin ya bayyana cewa an kai shi wani shagon POS inda aka tura masu kudi N153,000 daga asusun sa.

Saidai bayan tura kudin, dalibin yayi amfani da rasit din domin bada rahotan a shafin sada zumunta.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda na Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da zargin, yana mai cewa,“ gaskiya ne. ”

Oyeyemi ya kara da cewa an cafke jami’an uku kuma a yanzu haka suna fuskantar shari’a bisa dokar kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *