fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

An kama wata mata da ake zargi da kashe dan mijinta mai shekaru uku a Jihar Enugu

Jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin‘ yan sanda na 9 da ke jihar Enugu sun cafke Nnenna Egwuagu‘ yar shekaru 29 da haihuwa daga Umulumgbe a karamar hukumar Udi, a kan zargin yiwa dan mijinta mai shekaru uku allurar guba (Wisdom Egwuagu), wanda haka yayi sanadin mutuwarsa.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwe ya fitar, ta ce mijinta kuma mahaifin yaron, Justine Egwuagu, wanda ya kai rahoton lamarin ga’ yan sanda, ya yi zargin cewa allurar guba da matarsa tayi wa yaron shi ne yayi sanadin mutuwarsa.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ta amsa cewa lallai tayi masa wannan allurar gubar.

Ta yi ikirarin cewa abin da ta yi ya biyo bayan gazawar mijinta ne na kula da ita da ‘yarsu; da kuma cewa tana son yaron ya kamu da rashin lafiya don mijinta ya kashe kuɗi sosai don yi masa magani.

An tabbatar da mutuwar yaron a asibiti kuma an ijiye gawar sa a dakin ijiye gawarsa don gudanar da bincike. ”

Ndukwe ya ce an gano kwantenar da ke dauke da sinadarin gubar da ta yi amfani da shi wajen yi wa yaron allura, yayin da ake ci gaba da gudanar da cikakken bincike a kan lamarin a CID ta jihar, Enugu.

Ya kara da cewa, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Ndatsu Aliyu, yayin da ya ke bayyana aikin a matsayin rashin hankali da takaici, ya shawarci ma’aurata da su kaunaci juna da gaske, su zauna lafiya ba tare da cutanawa daya ba kuma su yi amfani da duk wata hanyar doka domin magance matsalolin zamantakewarsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *