fbpx
Thursday, April 22
Shadow

An kama wata mata da maza biyu dake aikawa mutanen sakon barazana su bada kudi ko a yi garkuwa dasu a Adamawa

‘Yansanda a jihar Adamawa sun kama mutane 3 ciki hadda wata mata dake aikawa mutane sakon wayar hannu suna musu barazanar su biya kudin fansa ko kuma a yi garkuwa dasu.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Sulaiman Yahya Nguroje ya tabbatar da kamen inda ya bayyana sunayen wanda aka kama da Zainab Ahondu me shekaru 50, Sulaiman Adamu me shekaru 34, Sai Abdullahi Ayuba me shekaru 36.

 

Yace an kamasu ne bayan samun bayanan sirri kuma yanzu haka ana cikin bincikensu.

 

A baya dai hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka kama dan shekaru 70 dake kaiwa Boko Haram kwaya

 

Ana yawaitar samun garkuwa da mutane musamman a Arewacin Najeriya inda ake raba mutane da makudan kudade wajan ganin sun tseratar da danginsu, a wasu Lokutan ana rasa rayuka.

 

Investigations so far revealed that the suspects always extort their victims upon text messages threatening to kidnap them if certain amount is not paid.” he stated.

 

“The State Commissioner Police, Aliyu Adamu Alhaji, while commending OC SIB and his men for making it difficult for those criminals to escape arrest, equally directed further investigations into the case to bring up more Human and Material evidences for proper prosecution.” he added.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *