fbpx
Thursday, December 2
Shadow

An kashe fitaccen dan bindigan da ya taɓa ƙone wata mace a Zamfara

An kashe wani fitaccen ɗan bindiga a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Damina, wanda yake da sansani a dajin Kuyanbana a yankin Dansadau da ke yankin karamar hukumar Maru, wanda rahotanni suka ce ya taɓa ƙona wata mata da ranta.

Jaridar Daily Trust da ta ruwaito labarin ta ce ya mutu ne sakamakon faɗan da ɓangarensa ya yi da ɓangaren wani ɗan bindigar Dogo Gide.

Jaridar ta ce Damina ya sha kai munanan hare-hare da satar mutane da satar shanu a garuruwa da dama yankin Dansadau.

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji a fadan da aka yi a kusa da Chilin da Fammaje,wasu al’ummu biyu da ke karkashin ikonsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *