fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

An kashe Manoma 12 da wasu 10 a Jihar Zamfara

Wau rikici daya kaure a Magami dake mayaba a Gusau ta jihar Zamfara yayi sanadiyyar mutuwar Manoma 12 da jikkata aasu 9.

 

Maharan sun farwa Manoman ne yayin da suka je sharar gona dan shiryawa damunar bana. Hakana maharan sun tafi da shanu da dama.

 

An yi jana’izar wanda aka kashe kamar yanda addinin Musulunci ya tanada. Hakanan a wani lamarin me kama da wannan, an kai hari a Barki dake Girkau na karamar hukumar Anka.

 

Maharan sun je da misalin karfe 9 na ranar Alhamis inda suka rika harbin kam mai uwa da wabi tare da kashe wasu mutane 10, kamar yanda Channels TV ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *