fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

An kashe masu satar mutane biyu, an kame wasu a Jihar Kogi

Jami’an tsaro na NSCDC a wani samamen hadin gwiwa tare da mambobin kungiyar ‘yan sintirin yankin sun cafke wasu gungun masu satar mutane da ke addabar matafiya a kan hanyar Idah-Ajegu a jihar Kogi.

An tattaro cewa tawagar yan sintirin sun yi karo da masu garkuwar yayin da suke tsoratar da matafiya akan hanya a ranar Asabar, 1 ga watan Mayu.

Jami’an tsaron sun shawo kan masu garkuwar, inda suka kashe biyu, sun kuma kam biyu tare da kubutar mutanen biyu daga hannun su.

Babban sakataren labarai na gwamnan jihar Kogi, Muhammed Onogwu, wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ga manema labarai, ya ce Yahaya Bello ya umarci shugabannin kananan hukumomin, hukumomin tsaro, ‘yan banga, mafarauta da sauran jama’a da su yi aiki tare cikin hadin kai don kawar da masu aikata laifi daga jihar.

Gwamna Bello ya yi gargadin cewa jihar ba waje ne da ake aikata ayyukan assha ba kuma tabbas za a hukunta wadanda suka aikata laifuka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *