fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An kashe mutane 2 a Kaduna, 1 a Jos, Dansanda 1 a Katsina

‘Yan Bindiga sun kashe mutane 2 a Mazari dake Buruku, Karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna.

 

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka ga manema labarai a yau, Talata.

 

Wadanda aka kashe din sune,Mariya Sale da Bitrus Luka sannan an jikkata mutane 6.

 

A jihar Katsina kuma ‘yan Bindigar sun kashe dansanda ne a Kauyen Ruma karamar hukumar Batsari inda suka kuma shiga Wani Kauyen Ruma dake karamar hukumar Batsari inda suka kaiwa Tawagar ‘yansanda 10 harin kwantan bauna.

 

‘Yan Bindigar da suka kai harin sun kai su 100. ‘Yan Bindigar  sun fito ne daga jihar Zamfara.

 

A jihar Filato kuma sun kashe Dakup Nteim da jikkata matarsa, Blessing.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *