fbpx
Friday, May 14
Shadow

An kashe mutane 21:Gwamnoni da Sanatoci sun roki Shugaba Buhari a kawo karshen matsalar tsaro yayin da Boko Haram ta kafa sansani kusa da Abuja

A jiya, Talata mutane 21 ne aka kashe a fadin Najeriya, kamar yanda Rahotanni suka nunar. Kuma ciki hadda jami’an tsaro.

 

Majalisar Dattijai ta tattauna akan lamarin inda ta nemi a dauki matakin kawo tsaro, Sanata Sani Musa daga jihar Naija ne ya dauki nauyin kai maganar majalisar.

 

Hakan na zuwane yayin da Boko Haram ta kafa tuta a garin Kawure dake kusa da Abuja.

 

Gwamnonin Benue, Samuel Ortom dana Borno, Babagana Umara Zulum, dana Naija, Abubakar Bello dik sun yi kira ga Shugaban kasar a kawo karshn matsalar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *