fbpx
Saturday, January 22
Shadow

An kashe mutane 45 a Nasarawa, Shugaba Buhari yace ya kadu sosai

Manoma 46 ne aka kashe a jihar Nasarawa bayan ballewar rikici tsakanin manoman da makiyaya a jihar.

 

Lamarin ya farune a kananan hukumomin Lafiya, Obi da Awe. Hakanan a baya ma an kashe akalla Makiyaya 20 a yankin.

 

A sakon ta’aziyyar sa ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu, Shugaba Buhari ya bayyana cewa yayi Allah wadai da lamarin.

 

Shugaban yace yana bayar da tabbbacin ba zai yi kasa a gwiwa ba sai ya ga cewa, yayi maganin wannan matsala da kuma gano wanda ke wannan aika-aika dan hukuntasu.

 

Yace lamarin ya sosai mai rai sosai, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *