fbpx
Saturday, June 19
Shadow

An Kashe Mutane 51 A Sabbin Hare-Haren Jihar Zamfara

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe a kalla mutane 51 a wasu hare-hare da suka kai kan kauyuka shida a karamar hukumar Zurmi da ke jihar ta Zamfara.

Garuruwan sun hada da Kadawa, Kwata, Maduba, Ganda Samu, Saulawa da Askawa.

Daruruwan mazauna ne suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren, inda da yawansu, ciki har da mata da yara kanana, suka fake a garuruwan Dauran da Zurmi.

Mazauna yankin sun ce wasu mutane dauke da muggan makamai a kan babura sun afkawa garuruwan, suna kashe mutane.

“Mahara sun yi ta bin mazauna cikin gidajensu zuwa gonaki suna kashe su,” in ji wata majiya.

An riga an gano gawarwakin mazaunan da aka kashe a sabbin hare-haren kuma an kawo su zuwa Dauran, wani gari da ke kusa da kilomita 10 yamma da garin Zurmi, hedkwatar karamar hukumar Zurmi.

“Har yanzu ba a gano sauran gawarwaki da yawa daga cikin dajin da ke kewaye ba duk da cewa ana kokarin dawo da su don a binne su yadda ya kamata.”

“Akwai tsoron kar masu dauke da makamai su dawo su kashe wadanda ke yin jana’izar. Wannan shine dalilin da yasa muka yanke shawarar kai gawawwakin mutanen Dauran.

“Zuwa yanzu, mun binne mutum 28 da abin ya shafa a cikin al’umma. Kamar yadda nake magana da ku, mun gama ayyukan jana’izar. An yi jana’izar mutanen da abin ya rutsa da su, ”kamar yadda wani mazaunin garin mai suna Haruna ya shaida wa Aminiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce‘ yan sanda sun kawo gawarwaki 14 domin yi musu jana’iza a makabartar Unguwar Gwaza da ke Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Mista Hussaini Rabiu, yana garin Dauran.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *