fbpx
Saturday, December 4
Shadow

An kashe mutane 7, da dama sun jikkata a wani hari a jihar Adamawa– Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da aka kai a unguwar Negga da ke karamar hukumar Numan a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), DSP Yahaya Sulaiman Nguroje, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Al’ummar Negga na karkashin gundumar Bolki ne a karamar hukumar Numan, wani kauye mai iyaka tsakanin jihar Adamawa da Taraba.

“An ce an kashe mutane bakwai, wasu bakwai kuma sun jikkata.

“An yi imanin cewa wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai harin,” in ji PPRO.

Rundunar ‘yan sandan dai ta tura wata runduna ta musamman a yankin, yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Numan domin yi musu magani.

A cewar Nguroje, hukumar da ke binciken manyan laifuka (CID) ta dauki matakin zakulo maharan.

Rundunar ‘yan sandan ta bukaci jama’a da su rika taimakawa rundunar a kodayaushe da bayanai masu amfani wajen dakile matsalar rashin tsaro.

A halin da ake ciki, Majalisar Dokokin Jihar ta yi Allah-wadai da harin, ta hanyar gabatar da kudirin da dan majalisa mai wakiltar yankin, Hon. Pwamwakeno Mackondo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *