fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

An kashe mutum daya yayin da ‘yan bindiga suka kai hari Zamfara, inda suka cinnawa wata kasuwa wuta

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan fashi ne, a jiya sun bude wuta a Kasuwar Yartashar Sahabi, karkashin Masarautar Dansadau da ke cikin Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum daya, suka jikkata da yawa, sannan suka cinna wa kasuwar wuta.
Wani ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan fashin sun mamaye dandalin kasuwar, inda suka fara harbi a lokaci-lokaci a iska.
Ya bayyana cewa yayin harin, mutane da yawa sun ji rauni yayin da suke kokarin tserewa daga hannun ‘yan fashin.
A cewarsa, wasu mazauna garin sun kulle kansu a cikin gidajensu, yayin da ‘yan fashin suka tafi da kayayyakin abinci na miliyoyin nairori mallakar‘ yan kasuwar, daga nan suka cinna wa kasuwar wuta.
“Yan fashin bayan sun wawushe wasu kayayyakin abinci sun cinnawa kusan duka rumfunan kasuwar, ciki har da wasu kayayyakin’ yan kasuwa wuta suka gudu zuwa daji yayin da suka ga ‘yan sanda na zuwa da ke aiki da Operation Puff Adder,”
A halin yanzu, kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) na rundunar’ yan sanda na jihar, SP. Muhammad Shehu ya tura yayin da layin wayarsa ke kashe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *