fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An Kashe Shi Ta Hanyar Banka Masa Wuta Sakamakon Zagin Annabi S.A.W Da Ya Yi A Jihar Bauchi

Daga Shuaibu Mai Swansea

Wani matashi mai suna Talle Mai Ruwa ya yi batanci ta hanyar zagi gadan-gadan ga Fiyayyen Halitta Annabi Mohammad S.A.W a garin Sade dake karamar hukumar Darazo, wanda hakan ya sanya bacin rai ga musulman cikin garin, inda suka aiwatar da hukuncin kisa kai tsaye ba tare da sauraron hukuncin gwamnati ba.

 

Matashin kafin ya aiwatar da wannan aika-aika musulmi ne da yake zaune a unguwar Kudun Sade, kuma kafin tabbatar da yin wannan hukuncin da mutanen gari suka yi malaman addinin musulunci sun kira shi sun tambaye shi akan abun da ake tuhumarsa, a take ya amsa musu da cewa ya aikata, wannan dalilin ya sa mutane gari suka aika shi izuwa barzahu.

 

 

 

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *