fbpx
Thursday, December 2
Shadow

An Kashe Shi Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wurin Zagayen Maulidi A Garin Mararraba/Nyaya

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

Wani magidancin matashi ya rasa ransa a ranar Talatar da ta gabata, sakamakon burma masa wuka a kirji da wani matashi ya yi a yayin da ake kan zagayen maulidi domin murna da zagayowar ranar da aka haifi Annabi SAW a garin Mararraba/Nyaya, wato iyakar Abuja da jihar Nasarawa.

Mamacin mai suna Muhammad Sani, wanda dan agaji ne, kuma yana aikin banga tare da yin saukale a kasuwar ‘Yan Lemo dake garin Mararraba/Nyaya, ya gamu da ajalin nasa ne jim kadan da isowar sa bakin hanya inda dandazon al’ummar musulmi ke zagayen maulidin bayan dan acaban da ya dauko sa ya sauke shi.

Bayan Muhammad Sani, wanda ya rasu ya bar mata daya da ciki (haihuwa ko yau ko gobe) ya tsallako titi domin shiga cikin dandazon masu zagayen mauludin, inda shigar sa cikin jama’ar ke da wuya, sai ya ga an biyo wani matashi ana zargin sa da satar waya, inda yana rike matashin, kawai sai ya fallo wuka ya daba masa a kirji, inda nan take ya zube a kasa shi kuma barawon ya shiga cikin rububin mutane ya gudu.

Saidai abin da ya daurewa jama’a kai game da lamarin shine, yadda matashin da ya yi kisan ya sha duk da cewa a cikin dandazon al’umma ya aikawa wannan ta’asar.

Saidai a yayin jin ta bakin jami’an tsaro, kakakin ‘yan sandan garin Mararraba, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa suna neman wanda ya aikata laifin ruwa a jallo, duk da cewa ya yi layar zana, inda da zarar sun cika hannu da shi zai fuskanci hukuncin da ya kamace shi.

Tuni dai aka yi jana’izar mamacin a gidansa dake Rugar Bayero a bayan kasuwar ‘Yan Lemo a garin na Mararrabar jihar Nasarawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *