fbpx
Friday, April 23
Shadow

An Kashe Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah A Nasarawa

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Nasarawa, Alhaji Mohammed Hussain.
An kashe Hussain tare da shugaban kungiyar a karamar hukumar Toto, Mohammed Umar, a daren Juma’a.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Nasarawa, Ramham Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
“A ranar 2/4/2021 da misalin karfe 7 na yamma, an samu labarin cewa wasu‘ yan bindiga da ba a san ko su wane ba ne wadanda ake zargin Fulani ne ’yan bindiga sun kai hari tare da kashe wani Mohammed Hussaini, Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Jihar Nasarawa da Mohammed Umar, Shugaban kungiyar a karamar hukumar Toto a kasuwar Garaku.
“Bayan samun labarin, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Bola Longe ya hanzarta tura jami’an Operation Puff Adder II zuwa wurin da aka gano gawarwakin biyu kuma aka kai su asibiti,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *