fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An kashe yan bindinga 8 kuma an kwato makamai a Katsina – Hukumar Yan Sanda

Tawagar jami’an tsaro sun kashe mutane takwas da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina

Kakakin rundunar ‘yan sanda SP Gambo Isah, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin a Katsina.

Yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji, sun kai farmaki sansanonin ’yan bindiga a bayan garuruwan Guzurawa da Garin-Gamboi, duk a karamar hukumar Safana ta Katsina.

Samamen ya samu nasara a yayin da rundunar ta kashe‘ yan fashin guda takwas, ta kone babura tara, sannan ta kwato bindiga kirar AK 47 guda daya tare da harsasai masu rai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *