fbpx
Thursday, April 22
Shadow

An kashe yan sanda 3 yayin da wasu yan bindiga suka kai hari kan tawagar sintiri a Akwa Ibom

Yan sanda uku sun mutu bayan wasu da ake zargin’ yan bindinga ne, sun kai musu hari a karamar hukumar Essien Udim da ke jihar ranar Laraba 31 ga Maris.

Ben Ajide, wani babban Sufeton ‘yan sanda (CSP) kuma kwamandan sashin kai dauki na rundunar’ yan sanda a Akwa Ibom na daga cikin jami’an da aka kashe a harin.

Odiko MacDon, jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce har yanzu ba a ga wasu jami’ai 4 ba.

Ya kara da cewa duk da ba a san musabbabin faruwar wadannan hare-haren, ba tare da bata lokaci ba, an fara gudunar da bincike domin kame da hukunta yan ta’addan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *