fbpx
Monday, May 10
Shadow

An Kori Iyayensu daga aiki, An kuma kara Kudin Makaranta, Bamu yadda ba>>ASUU kan karin kudin jami’ar Kaduna

Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU reshen jami’ar Jihar Kaduna, KASU sun bayyana cewa, basu basu amince da karawa Daliban kudin makaranta ba.

 

Shugaban kungiyar, Peter Adamu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

 

Yace kaso 75 cikin 100 na daliban ka iya hakura da Karatun idan aka nace lallai sai sun biya wafancan makudan kudade.

 

Yace an kori ma’aikata daga aiki wanda yawanci iyayen wadannan dalibai na ciki, kuma yanzu an kara musu kudi, yace kuma mafi yawancin daliban ‘ya’yan manoma da makiyayane.

 

Ya nemi gwamnatin ta sake Duba lamarin da an saukakawa al’umma. Ya kuma yi kira ga masu fada aji irinsu Sarakuna da sauran Shuwagabannin Al’umma su Shiga lamarin dan a saukakawa mutane.

 

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa, kumgiyar ta kara da cewa ana sane da rage ma’aikata da kuma matsin tattalin arzikin da Coronavirus ta kawo dan haka wannan kari sam bai kamataba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *