fbpx
Saturday, April 17
Shadow

An Kubutar da 5 daga cikin dalibn Kaduna da aka sace

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da Gwamnatin Jihar Kaduna cewa an gano biyar daga cikin 30 da suka yi saura a daliban Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation da aka sace a watan jiya.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar ta wallafa a shafnta na Twitter tace daliban na hannun jami’an tsaro domin tabbatar da lngancin lafiyarsu.

Sanarwar ta ce da zarar an samu wani karin bayani game da halin da ake ciki gwamnatin jihar za ta sanar.

A watan jiya ne aka sace dalibai da dama a wannan kwaleji to amma daga baya aka samu nasarar kubutar da wasu sama da 100 daga ciki.

Inda Sojojin Najeriyar suka ce sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130. Amma kuma a lokacin ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba, wadanda yanzu aka gano biyar daga cikinsu.

Hakan dai yana nufin har yanzu akwai sauar dalibai 25 a hannun ‘yan fashin dajin.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun daga watan Disambar 2020 .

“The Nigerian military has informed the Kaduna State government that five of the many kidnapped students of the Federal College of Forestry Mechanisation, Afaka, Kaduna were recovered this afternoon and are presently in a military facility where they are undergoing a thorough medical check-up.

“The Kaduna State government will provide updates on further operational feedback to be received on this case,” the statement read.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *