fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An kubutar da daliban Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya dake Jihar Benuwai ba tare da biyan kudin fansa ba

Daliban nan uku na Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya, Makurdi (FUAM) da ke jihar Benuwai, wadanda aka sace daga harabar makarantar sun sake samun ‘yanci.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda na Benuwai, Catherine Anene ya tabbatar da sakin nasu a ranar Laraba 28 ga Afrilu.

Anene ya ce an sako daliban a ranar Talata 27 ga Afrilu ba tare da an biya kudin fansa ba.

Rosemary Waku, daraktan labarai, yarjejeniya da hulda da jama’a na FUAM ita ma ta tabbatar da sakin daliban.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *