fbpx
Monday, November 29
Shadow

An kulle mawaƙin Kwankwasiyya bisa zargin ya tozarta matar Ganduje

MAWAƘInan da ‘yan sanda su ka kama a Katsina su ka kai shi Kano ana zargin sa ne da laifuffuka da su ka haɗa da aikata ɓatanci a kan iyalin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Talata mu ka ba ku labarin yadda ‘yan sandan su ka tashi takanas ta Kano su ka je Katsina su ka kamo mawaƙin siyasar mai suna Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waƙa, su ka tafi da shi Kano.
Wata majiya ta ce tare da amincewar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina aka kama Kosan Waƙa, wanda mawaƙin rundunar siyasar Kwankwasiyya ne wadda ke adawa da Ganduje.
A ranar Laraba aka gurfanar da shi a kotu mai lamba 72 da ke Nomansland a Kano, aka tuhume shi da sakin sabuwar waƙar sa mai taken ‘A Wanki Gara’ ba tare da sahalewar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba.
A kotun, an zarge shi da aikata ɓatanci ga Gwamnan Kano da iyalan sa, inda har aka faɗi inda ya ambaci kalmar “Gwaggo” a waƙar, wanda laƙabi ne na matar gwamnan, Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.
Wata tuhuma kuma ita ce yunƙurin tayar da tarzoma a cikin al’umma.
Bayan an karanta masa tuhumar da ake masa, Kosan Waƙa ya musanta zargin, ya na faɗin cewa shi ba da kowa ya ke ba, domin ai babu wanda ba ya da gwaggo.
Lauyan gwamnati, Barista Wada A. Wada, ya gabatar da shaidun da ake tuhumar mawaƙin a kan su.
Da lauyan da ke kare mawaƙin ya nemi a bada beli, sai Mai Shari’a Aminu Gabari ya ƙi.
A maimakon haka, sai ya tura mawaƙin zuwa gidan yari bayan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2020.
Bayan an tashi daga kotun, mujallar Fim ta tuntuɓi shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alh. Isma’il Na’abba (Afakallahu), game da lamarin, inda ya ce ba shi da hurumin da zai yi magana saboda maganar ta na kotu. “A jira abin da kotu za ta ce,” inji shi.
Wannan shari’a dai ta tada muhawara musamman a Katsina inda wasu ke ganin hukumar ta wuce gona da iri, su ka ce ba ta da hurumin da za ta kai kama wani wanda ba ɗan Jihar Kano ba ta kai shi Kano. 
Wani tsohon shugaban hukumar, wanda ya buƙaci a sakaya sunan sa kuma, ya ce: “Hukumar Tace Finafinai iya Kano ne kawai ta ke da hurumi. Idan mutum ba a Kano ya ke ba, ba ta da hurumin hukunta shi. 
Ya ce, “Sai dai idan ka yi abin aka kama ana sayarwa a Kano, za a nemi ɗan kasuwar da ka sayar masa ya nemo ka a gurfanar da ku a kotu baki ɗaya. 
“Misali, Gwamnan Kano zai iya magana da Gwamnan Katsina ya sa a nemo yaron a kan me ya sa ya yi waƙar? 
“Ko kuma hukumar ta kai shi ƙara a Katsina tunda a can ya yi laifin, wanda ya ke zargin an yi waƙar don shi sai ya bi kadin haƙƙin sa a can, idan an same shi da laifi za a iya ladabtar da shi. 
“Amma a je Katsina a kamo shi a kai shi kotu a Kano, babu wani sashe inda aka rubuta haka a dokar hukumar.”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *