fbpx
Monday, May 10
Shadow

An kwace Miliyan 25 da aka baiwa gurguwarnan ta Legas bayan gano cewa ta bada labarin karya

Guguwarnan ta Legas dake Tallar Ruwa a bakin Titi, Mary Daniel da aka tarawa Miliyan 25 bayan bayyanar labarinta, a yanzu tana tsaka mai wuya.

 

Ta dai bayar da labarin cewa, an yanke mata kafane dalilin wani hadarin mota da duka mutanen dake cikin Motar suka mutu amma ita ta tsira, sannan kuma ita marainiyace tana da diya da kuma kakarta da take kula dasu.

 

Lamarinta ya baiwa mutane tausai sosai inda akao ta taimaka mata. Saidai wadanda suka taimaka mata ta yi wannan karya sun rika matsa mata Lamba akan ta basu kasonsu na kudin da aka samu ko kuma su watsa maganar.

 

A karshe dai magana ta fito fili bayan an yi bincike inda aka gano cewa mahaifinta na da rai, kuma tun waja haihuwarta aka yanke mata kafa.

 

An kuma gano cewa har tsayuwar da ta yi a bakin titi tana tallar ruwa duk Shiri ne dan a samar mata taimako ne.

 

Hukumar ‘yansanda ta jihar, Tace an dauki matakin hana ta amfani da kudinne da kada lamarin ya zama gasa ga mutane su rika fitowa suna irin wannan abu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *