fbpx
Saturday, December 4
Shadow

An Mayar Da Gidan Karuwai Zuwa Katafariyar Islamiyya A Yankin Igabi Dake Jihar Kaduna

Wani abun ban sha’awa da yabawa ya faru a karamar hukumar Igabin jihar Kaduna, inda wani gidan mata masu zaman kansu ya zama katafariyar makarantar da za a cigaba da koyar da kananan yara a bangaren ilimin zamani da na addini a yankin kasuwar Daji da ke cikin karamar hukumar ta igabi.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da gidan, Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris, wanda Makaman Zazzau Alhaji Umaru Mijinyawa ya wakilta, ya gode ma Allah bisa nasarar da aka samu har aka sayi gidan daga hannun mamallakin sa, wanda sanadiyyar shine aka jima ana aikata miyagun laifuka a wannan gida.
Kuma ya bukaci mutanen yankin su godewa Allah saboda tsamo su da ya yi daga halin da suke ciki a baya
Ya kuma jinjinawa Hakimin gundumar Igabi da sauran sarakunan yankin bisa namijin kokarin da suka yi har aka kai ga samun wannan nasarar.
Makaman Zazzau ya Kara da cewa, jami’an tsaro sun samu labarin cewa wasu na shirya makarkashiya ga sabuwar makarantar da aka bude, sai dai ya yi kashedi ga duk wani mai nufin wannan makaranta da sharri ya guji aikatawa domin sam hukuma ba za ta bari ba.
Shi ma da yake jawabin sa a wurin taron, Hakimin gundumar Igabi Alhaji Abdulkadir Iya Fate, ya ce, tun a shekaru da suka gabata, aka fara kokarin karbar wannan gida daga mamallakin sa domin tsaftace shi daga kazamai da suka jima suna aikata badala da ma sha’a a wannan yanki. Duk da an samu kalubale matuka a lokacin karbar gidan, amma bisa taimakon Allah da kuma shuwagabannin al’ummar yankin, aka kai ga nasara, kuma aka siya wannan gida daga wurin mamallakin sa.
Ya kara da cewa, saboda kokarin amsar gidan, mutanen yankin sun yi zargin cewar za’a nakasa masu harkokin kasuwancin su, saboda yadda mutane ke shigowa daga garuruwa daban-daban domin aikata badala a gidan. Amma ya roke su dasu cire wannan tunani a Cikin ran su kuma su sa a ransu cewa, yanzu ne ma za su samu dukiya tsaftatacciya da zata taimaka wurin habaka tattalin arzikin yankin baki daya.
A jawaban malaman da suka halarci taron su daban-daban, irin su Sheikh, Dr, Muhammad Aliyu da Sheikh, Abubakar Jumare, sun yi addu’oi na musamman ga al’ummar yankin, kuma sunyi fatan aikin da suka yi ya zama sanadiyyar yafe kura-kuran da suka aikai a baya.
Sannan kuma ya godewa Allah bisa nasarar da aka samu kawo yanzu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *