fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

An mika daliban makarantar sakandare 4 ga ‘yan sanda a Calabar bisa zarginsu da shiga kungiyar asiri

Wasu daliban makarantar sakandaren Gwamnati hudu da ke garin Akim Qua, Calabar da ake zargin suna da alaka da kungiyar asiri da sauran munanan dabi’u an mika su ga rundunar da ke yaki da kungiyar asiri ta rundunar ‘yan sanda ta Najeriya don yi musu tambayoyi.

An mika daliban ga jami’an tsaro ne a cikin harabar makarantar.

Da yake magana a lokacin mika ragamar a ranar Juma’a, 5 ga Maris, Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Jihar Kuros Riba kan Ilimi, Kwamared Castro Ezama ya gode wa jami’an tsaro kan zuwa wajen a cikin lokacin, jim kadan bayan an tuntube su.

Kwamared Ezama a lokacin da yake zantawa da daliban makarantar kan duk wani nau’i na aikata laifuka, ya gaya masu cewa Gwamna Ben Ayade baya shan inuwa daya da yan kungiyoyin asiri, masu shan muggan kwayoyi da sauran munanan halaye, kamar yadda ya umarci daliban da abin ya shafa su gabatar da iyayensu don taron gaggawa tare da shugabannin makaranta da jami’an tsaro don karin haske.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *