fbpx
Monday, October 25
Shadow

An nemi shugaba Buhari ya rika biyan tubabbun Boko Haram dubu 25 duk wata

Wani limamin coci, Dr. Samuel Chukwuemeka Kanu-Uche ya nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya rika biyan wanda suka tuba daga Boko Haram da ayyukan ‘yan Bindiga 25,000 duk wata.

 

Ya bayyana cewa, yunwa da Talauci ne yasa matasa a Arewa shiga ayyukan ta’addanci.

 

Yace amma biyansu wadannan kudaden tallafin zasu taimaka wajan hanasu komawa ruwa.

 

Ya kuma bayar da shawarar a saka babban malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi cikin wanda zasu taimaka a kawo karshen matsalar, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *