fbpx
Thursday, September 23
Shadow

An rufe makarantun kwana a Adamawa saboda tsaro

Gwamnatin Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta rufe makarantun kwana 30 cikin 34 da ke fadin jihar saboda matsaloli na tsaro.

Sanarwar da kwamishiniyar Lafiya, Mrs Wilbina Jackson ta fitar na cewa an rufe makarantun daga yau Litinin har sai baba ta gani.

A cewar sanarwar an ɗauki wannan mataki ne la’akari da taɓarɓarewa lamuran tsaro musamman na ɗalibai a makarantu.

Adamawa na daga cikin jihohohin da ke fuskantar barazana daga hare-haren ‘yan bindiga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *