fbpx
Saturday, October 16
Shadow

An sace babban likita a jihar Adamawa

Mahara dauke da bindigogi sun yi garkuwa da wani babban likita a jihar Adamawa.

Likitan mai suna Abdurrahman Kawuyo, na zaune ne a karamar hukumar Yola ta Kudu kuma ya na aiki ne a asibitin gwamnatin tarayya dake Yola.
Maharan sun afka gidan likitan ne da daren lahadi inda suka arce da shi.
Bayan haka an bayyana cewa basu dauki komai ba daga gidan.
Shugaban kungiyar Likitocin reshen jihar Adamawa Tounde Elijah, ya bayyana cewa sun kai wa iyalan likitan gaisuwar Allah ya kyauta.
Bayan haka Elijah ya bayyana cewa tuni sun fara tattaunawa da maharan domin a samu a ceto likitan da suka yi garkuwa da.
” Wani ma’aikaci ne ya kira likitan domin tambayarsa wani abu game da aiki, sai kawai ya ji wani murya da ba na likitan ba. Daga nan sai maharan suka mika wa likitan wayar inda ya yi masa bayanin halin da yake ciki.
” Zuwa yanzu dai maharan suna neman naira miliyan 10 ne kudin fansa. Amma dai muna nan muna ci gaba da tattaunawa da su.
Jihar Adamawa na daga cikin jihohin dak fama da hare-haren mahara da masu garkuwa. ” Babu wanda tsira daga wadannan mutane. Abin sai dai Allah ya kiyaye. Masu sai da ruwa ne, ‘yan Kasuwa ne, yanzu ya kaiga likitoci ma waske wa ake yi da su domin a biya makudan kudin fasa a jihar,” In Elijah.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *