fbpx
Friday, May 14
Shadow

An sace tsohon sakataren jam’iyyar PDP a jihar Jigawa

Wasu mutane da ba a san su ba sun sace tsohon sakataren jam’iyyar PDP a karamar hukumar Auyo da ke Jihar Jigawa.
Adamu Digitawa, mai shekaru 64, an sace shi ne a ranar Talata da misalin 1:30 na safe a kauyen Aguza.
Majiyar ta bayyana cewa an sace shi ne bayan da ya biya kudin fansa ga wani dan uwansa da masu laifin suka sace.
Wannan na zuwa makwanni bayan sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Jigawa Isa Alhassan Koreyal ya mutu.
Ya rasu a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano bayan ya yi gajeriyar rashin lafiya.
Mai magana da yawun ‘yan sanda ASP Zubairu Nurraddeen ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun sace tsohon Sakataren na PDP a ranar Talata a kauyen Aguza.
Zubairu ya ce, ana nan ana ta kokarin ganin an kamo wadanda ake zargin tare da kubutar da shi.
Amma, ya bukaci dangin wanda aka sace din da su ba jami’an tsaro hadin kai tare da ba su da dukkan bayanan da suka dace wadanda za su kai su ga kubutar da shi lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *