fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An sace wa jarumin ‘Labari Na’ mota, kwana 1 da sayen ta

WASU ɓarayi sun auka gidan matashin jarumin finafinan Hausa Nasiru Naba jiya, su ka ƙwace motar sa da ya saya shekaranjiya.

Jarumin, wanda cikakken sunan sa Nasiru Bello Sani, ɗan wasa ne da ya fito a finafinai masu yawa, ciki har da shirin nan mai dogon zango na ‘Labari Na’ wanda tashar talabijin ta Arewa24 ke haskawa.

 

Iftila’in ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 zuwa ƙarfe 2:00 na daren jiya Talata, 30 ga Maris, 2021, lokacin da ‘yan fashin su ka auka gidan da ke unguwar Maidile da ke birnin Kano, ɗauke da bindigogi.

 

A game da yadda abin ya faru, Nasir Nava ya labarta wa mujallar Fim cewa: “Ina cikin barci sai na ji ana tattaɓa ƙofa, ana ƙoƙarin buɗe ta. Jin haka ya sa na farka.

 

“Sai na buɗe ƙofar ɗaki na, na zo falo na ga mutane a waje a tsaye, su na ƙoƙarin banƙare ƙofar falon.

 

“Sai na yi sauri na zo ina ƙoƙarin ba wa ƙofar tsaro, kar su ɓalla ta. To da su ka ga haka, sai su ka fara zuro mani kan bindiga.

 

“Haka dai su ka banƙare ƙofar, su ka shigo, su ka tsare ni da bindugu a kai na, da zummar sai na ba su kuɗi. Sannan fa sauran ‘yan fashin su ka fara bincikar ko’ina na gidan, su na duba kuɗi, don ban ma san sun ɗauki makullin mota ta ba, sai daga baya na gani. Kuma motar ma kwanan ta ɗaya da sayowa; su ka ɗauke ta da kuɗi da kamfuta ta da kuma wayoyi na da sauran wasu abubuwan amfani na.”

 

Sai dai Nasiru Naba ya ce ‘yan fashin ba su raunata ko ɗaya daga cikin iyalan sa ko shi kan sa ba.

 

Ya ce bayan tafiyar su, ya sanar da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano abin da ya faru domin su ɗauki matakin da ya kamata.

 

Wakilin mujallar Fim ya yi ƙoƙarin tuntuɓar kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma sai ya ji wayar sa a kashe.

 

Mu na addu’ar Allah ya kare aukuwar irin haka a nan gaba, ya kuma tona asirin waɗannan mutane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *