fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

An sace wasu ma’aurata daga suna cikin dakin kwanan su a Jihar Nasarawa

An sace ma’auratan ne a garin Ukya Sabo da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Wani shaidar gani da ido mai suna Samuel, ya shaida wa Aminiya cewa an sace Yohana Isheme da matarsa, Noami Yohana da misalin karfe 1 na dare a ranar Asabar 11 ga watan Yuli.

Ya ce masu satar mutanen da suka mamaye yankin da yawan mutane dauke da muggan makamai, suka kuma yi kwanton bauna a wurare daban-daban cikin yankin kafin wasu gungun mutane su ketara shinge gidan wadanda aka sace.

An kuma tattaro cewa suna yin harbi a iska lokaci-lokaci don tsoratar da makwabta yayin da suke jagorantar wadanda abin ya rutsa da su daga yankin zuwa cikin daji.

An gano cewa Isheme ma’aikaci ne a sashin lafiya a karamar hukumar Toto, yayin da matarsa ​​malama a makarantar firamare ta (LEA), dake yankin Tika.

Shugaban sashin bayanai na karamar hukumar Toto, Mista Gabriel Hagai ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *