fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

An sake nada Amina J. Muhammad a matsayin mataimakiyar sakataren majalisar Dinkin Duniya a karo na 2

Sakataren majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya sake nada ‘yar Najeriya, Amina J. Muhammad a matsayin mataimakiyarsa a karo na biyu.

 

A ranar Juma’a ne dai aka sake nada Antonio Guterres a matsayin sakataren majalisar a Karo na 2 wanda kuma wa’adin nasa zai fara ne daga 1 ga watan Janairu na shekarar 2022 zuwa shekaru 5.

 

Guterres bayan nadinsa ya ce shima ya nemi Amina ta zama mataimakiyarsa a karo na 2 kuma yana fatan zata amince.

 

Da take bayar da nata jawabin, Amina tace ta amince da wannan girmamawar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *