fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An sake sace dalibai a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu dalibai a lokacin da suka kai hari a wata jami’a mai zaman kanta a jihar Kaduna.

An kai harin ne a daren Talata kuma har yanzu ba a san adadin daliban da aka sace ba.
Makarantar, Green Field University, tana kan babbar hanyar Kaduna – Abuka a cikin karamar hukumar Chikun.
Hakanan ita ce jami’a mai zaman kanta ta farko a jihar kuma an kafa ta shekaru uku da suka gabata.
Lamarin na baya-bayan nan shi ne babban hari na farko da ‘yan fashi suka kaddamar kan al’ummomin da ke kusa da titin Kaduna zuwa Abuja tun lokacin da aka tura sojoji mata 300 zuwa yankin a watan Janairun wannan shekarar.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan Talabijin na Channels.
A cewar shaidun gani da ido, ‘yan bindigar sun kutsa cikin jami’ar ne a daren jiya kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi, kafin su tafi da wasu daga cikin daliban.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *