fbpx
Friday, May 14
Shadow

An saki basaraken gargajiya da aka sace a Jihar Ekiti

Basaraken gargajiyar, David Oyewunmi da aka sace ya samun yanci bayan ya kwashe kwanaki biyar a tsare.

A kwana baya mun ruwaito maku cewa an sace Oyewunmi ne a ranar 16 ga Afrilu a fadarsa bayan ‘yan bindigar sun ketara katangar fadar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na Ekiti, Sunday Abutu wanda ya tabbatar da cewa an saki sarkin ya kara da cewa a yanzu haka yana karbar kulawar likita a wata cibiyar kiwon lafiya da ke cikin jihar sakamakon halin kuncin da ya fuskanta a hannun masu satar mutanen.

Abutu ya alakanta sakin sarkin da hadin gwiwar ‘yan sanda da jami’an tsaro na jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *