fbpx
Sunday, September 26
Shadow

An sako ma’aikatan gona uku da aka sace wadanda suke yiwa Obasanjo aiki

Ma’aikata uku da ke aiki da tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, an sake su kwanaki biyu bayan sace su.

An yi garkuwa da masu aikin gonar a kewayen yankin Kobape na jihar Ogun da misalin karfe 6 na yamma a ranar Laraba 8 ga watan Satumba.

A yammacin Juma’a, 10 ga watan Satumba, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da kubutar da mutanen, inda ya ce an sake su ba tare da sun biya kudin fansa ba.

A cewar Oyeyemi, masu garkuwar ba su da wani zabi illa sakin ma’aikatan yayin da jami’an rundunar masu yaki da garkuwa da mutane da kuma SWAT suka matsa musu.

Oyeyemi ya kara da cewa, jami’an nan da nan bayan faruwar lamarin, sun shiga daji, suna kara matsa lamba ga masu garkuwa da mutanen.

Ya ce, masu garkuwar da yammacin jiya, sun sake su ba tare da sun ji rauni ko biyan kudin fansa ba.

Sai dai yace jami’an har yanzu jami’an basu kama mutum ko daya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *