fbpx
Monday, November 29
Shadow

An samar wa mata kofin yin fitsari don hana kamuwa da cuta

Wata mata ‘yar kasar Kenya ta samar da wata mafita ga masu fama da irin cututtukan da ake kamuwa da su bayan amfani da bandakunan da ba su da tsafta.

Njeri Muthaka tana sayar da kofuna da ke taimaka wa mata yin fitsari a tsaye, ba tare da sun tsuguna ba don kare su daga zama kan shadda mara tsafta da za su iya daukar kwayoyin cuta.
Ms Muthaka ta shaida wa BBC Swahili cewa ta sayo kofunan yin fitsarin ne daga wata kasa bayan da ta yi fama da cututtukan da suka shafi al’aura da mafitsara ba sau daya ba ba sau biyu ba.
Bayan da ta yi amfani da kofin ta kuma ga muhimmancinsa wajen hana ta sake kamuwa da cutar, sai ta anke shawarar sayar da kofunan.
Likitoci sun yi amanna cewar kofin fitsarin zai rage kamuwa da cututtuka. Wani likita Chris Obwaka ya ce: “Idan har ba kya zama a kan shadda ta gama-gari don yin fitsari, hakan zai iya rage hadarin kamuwa da cututtuka.
”Amfani da kofin zai taimaka sosai.”
Sai dai mazan Kenya na cewa amfani da kofin ya kauce wa tsarin al’adunsu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *