fbpx
Saturday, December 4
Shadow

An samu gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a Kano

‘Yan sanda a Najeriya sun tabbatar da samun gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a dakin girki a wani gida da ke wata unguwa a jihar Kano.
Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Laraba.
‘Yan sandan sun ce babu tabbacin dalilin mutuwar tasu, amma sun mika gawar zuwa asibiti don gudanar da bincike kan abin da ya haddasa mutuwar tasu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sai dai wasu daga cikin mazauna unguwar ta Badawa da abin ya faru sun bayyana cewar gidan da masoyan biyu suka mutu ba gidansu budurwar ba ne.

Wasu rahotanni na cewa kwanaki kadan ya rage a daura musu aure.

Amma iyayen namijin sun ce bisa ga yadda suka samu labarin, hayakin inji ne ya yi sanadiyar mutuwarsu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *