fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An tarawa Dansanda Dubu dari biyar bayan da wani farar hula ya lakada masa duka duk da yana rike da bindiga amma bai yi komai ba

‘Yan Najeriya da dama ne ke yabawa halayyar da wani dansanda ya nuna bayan da wani farar hula ya lakada masa duka.

 

Dansandan me suna, Sunday Erhato me mukamin ASP ya tare wata mota da ta yi aron hannu a Oniru dake Legas.

Saidai bayan tare motar, wani me suna Victor da abokin tafiyarsa dake cikin motar, sun fito inda suka fara cin zarafin dansandan, har sai da ya jikkata.

 

Saidai wani abin birgewa shine duk da wannan abu da aka ma dansandan bai dauki matakin ramuwa ba ko yin harbi da bindiga.

 

Kakakin ‘yansandan jihar ya bayyana cewa, an kama babban wanda ya aikata laifin inda abokin aikata laifib nashi ya tsere, sannan kuma a kama motar da suke ciki. Yace kwamishinan ‘yansanda ya jinjinawa halin dattakon da dansandan ya nuna inda kuma yayi kira ga sauran abokansa su yi koyi dashi.

 

Tuni dai wasu suka fara tara kudi wanda a yanzu sun kai Naira 500,000 dan tallafawa dansandan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *