fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

An kama wanda suka yi barazanar yin maganin wata mata da tawa Addinin Musulunci batanci a kasar Faransa

Wata kotu a Faransa ta sami mutane goma sha daya da laifin aika sakonnin batanci ga wani matashi Bafaranshe wanda ya yada faifan bidiyo na sukar addinin Islama a yanar gizo.

Bayan Mila (tana da shekaru 16 a lokacin) wani musulmi mai rubutun ra’ayin yanar gizo ya kirata da “‘yar madigo, kazama” saboda tayi magana game da jima’i a Instagram sai ta sanya wani hoto akan Instagram tana sukar addinin Islama.

Ta bayyana Musulunci a matsayin “addinin kiyayya” wanda ya sanya ana mata barazanar kisa da yawa.

Shugaban Kasar Macron ya goyi bayan matashiyar Inda yace a kasar Faransa kowa nada yanci batacin ga wani addini.

Mila, yanzu tana da shekaru 18 an tilasta mata ta fice daga makaranta kan cin zarafin kuma yanzu tana rayuwa karkashin kariyar yan sanda na awa 24.

A ranar Laraba, 7 ga watan yuli, an yankewa wadanda ake tuhuma 11 hukuncin daurin rai da rai saboda cin zarafinta ta yanar gizo kuma don haka za su yi zaman kurkuku ne kawai idan an same su wasu laifuka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *