fbpx
Saturday, October 16
Shadow

An yi garkuwa da jami’an kwastam 4 a jihar Katsina

‘Yan bindiga a jihar Katsina sun yi garkuwa da jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam su 4 tare da wasu sauran matafiya. Lamarin ya farune akan titin zuwa Batsari-Jibia.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

‘Yan Bindigar sun kwacewa jami’an na kwastam makamai inda suka tarkatasu tare da sauran wasu matafiya suka yi garkuwa dasu.

Lamarin ya farune a jiya, Laraba da misalin karfe 10 na safe inda ‘yan bindigar suka bayyana a kan babura da yawa.

Punch tace ta tuntubi me magana da yawun hukumar ta Kwastam a jihar Katsina, Peter Duniya amma yace ba zai iya cewa komai akai ba saboda yana hutu. Hakanan wasu jami’an kwastam dake bakin aiki sun bayyana cewa sun san da lamarin amma ba zasu iya cewa komai akai ba.

‘Yan bìndiga dai har ila yau sun kai wani harin wani gidan Kallo dake Magama inda suka kashe wasu matasa 2.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *