fbpx
Thursday, September 23
Shadow

An yi garkuwa da uba da dansa yayin da ‘yan bindiga suka shiga wani gida a Abuja

Wasu ‘yan bindiga da suka shiga wani gida a Abuja, sun yi garkuwa da wani Abdullahi Benda, da dansa mai shekaru 23, Jibrin Abdullahi Benda.

Lamarin ya faru ne a kauyen Yangoji da ke karamar hukumar Kwali a Abuja da sanyin safiyar Juma’a 3 ga watan Satumba.

Wani makwabci mai suna Zakari ya ce masu garkuwar sun ketara katangar gidan wanda abin ya rutsa da su, suka lalata kofofin da karfi, suka shiga cikin daki suka yi awon gaba da mutumin da daya daga cikin ‘ya’yansa.

Zakari yace; “A zahirin gaskiya, daya daga cikin masu garkuwa da mutanen yana tsaye a kan taga a bayan dakinsa yana harbi sama, saboda shinge ne ya raba shi da wanda aka sace.

“Sauran‘ yan kungiyar sun tsallake katangar suka shiga gidan.

“Sun yi kokarin awon gaba da matar mutumin, amma daga baya sun kyaleta bayan sun gano cewa tana shayar da jariri.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, ASP Daniel Y. Ndiparya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar na kokarin ganin an ceto wadanda aka sace da ransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *