fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

An yi yunkurin fasa gidan yarin Kano

Jami’an tsaro a jihar Kano sun dakile yunkurin fasa gidan yarin Kurmawa dake kusa da gidan sarkin a jiya, Alhamis.

 

Musbahu Lawal Kofar Nasarawa wanda shine kakakin hukumar a Kano, ya bayanawa manema labarai cewa, wasu wanda suke jiran hukuncin kisa ne suka tayar da fitinar.

 

Yace amma sun yi nasara dakile lamarin.

 

Yace dalilin tashin-tashinar saboda yanda aka kwace wasu miyagun kwayoyine da aka gano a hannun masu laifin da ake tsare dasu. Yace maganar wai rashin abinci ko rashin kyawun abincinne ya kawo wannan lamari ba gaskiya bane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *