fbpx
Monday, November 29
Shadow

An yiwa Mikel Obi Kalaman Wariyar Launin Fata

Kungiyar kwallon kafa ta Trabzonspor da ke babbar gasar kasar Turkiya ta caccaki kalaman wariyar launin fata da aka yi wa dan wasan tsakiyarta, kuma tsohon dan wasan Chelsea, dan Najeriya John Mikel Obi, biyo bayan nasararta kan Fenerbahce ranar Asabar da ta gabata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

An yi ta yi wa dan wasan mai shekaru 32 kalamai na wariyar launin fata a dandalin sadarwar intanet bayan doke Fenerbahcen 2-1 da ya kai Trabzonspor din matsayi na 3 a teburin gasar ta Turkiya.

Kungiyar ta ce ta shigar da wadanda suka aikata wannnan abin assha kara a kotu.

Kungiyar ta hau shafinta na twitter tana cewa”wariyar raunin fata dabi’a ce ta jahilai da marasa kan gado.”

Shi ma abokin wasan Mikel a kungiyar Trabzonspor, Joao Pereira ya shiga shafinsa na Twitter yana cewa wariyar launin fata ba abu ne da za a lamunta ba, kuma kwallon kafa ta fi wadannan kananan mutanenmasu wannan dabi’a mai ban takaici.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *